Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sojoji sun hallaka kwamandojin Boko Haram a Borno

Published

on

Rundunar sojin operation lafiya dole ta bayyana cewar ta hallaka wasu manyan kwamandoji na kungiyar Boko Haram da ISWAP, yayin wata arangama da suka yi a yankin arewa maso gabashin kasar nan.

Babban jam’in rundunar mai lura da harkokin yada labarai Manjo janar John Enence ne ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar a jiya Lahadi a Abuja.

Yace, sojojin sun kashe ‘yan kungiyar ta Boko Haram guda 6 a kauyen Kolofata dake kan iyakar Najeriya da Kamaru lokacin da suke kan hanyar su ta shiga dajin Sambisa.

Ya kuma ce, sojojin sun kwace wata wasika da aka rubuta da harshen Hausa, ake shirin mika ta ga wani mai suna Abu Fatima wanda guda ne daga cikin manyan kwamandojin kungiyar.

Karin labarai:

Harin kwanton bauna ya kashe sojoji da dama a jihar Katsina

Sojoji sun kara hallaka ‘yan bindiga a Zamfara

Sanarwar tace a cigaba da fafarar da sojojin ke yiwa maboyar yan kungiyar a yankin a Arewa masu gabashin kasar nan, sun hallaka karin kwamandoji guda 8 a kokarin su na kutsawa cikin san-sanin sojojin dake Damasak.

Ya kara da cewa, yawan samun sauyin shugabanni da kungiyar ta ISWAP ke yi, wata yar manuniya ce da ke nuna cewar sojoji, sun samo lagon su.

Yanzu haka dai tuni aka binne gawarwakin kwamandojin a kauyen Goski dake yankin.

Kwamandojin da aka hallaka sun hada da Tumbin Dabino Ba Issoufo, da tumbin Bororo Amir Batam da sauran su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!