Kiwon Lafiya
Kungiyar dalibai NAKSS ta nada sabbin shugabanni
Sabon shugaban kungiyar dalibai ‘yan asalin jihar Kano NAKSS reshen jami’ar Bayero a nan Kano Kwamred Musa Usman Sani, ya jaddada kudurin sa na kawo karshen matsalolin da suka dabai-baye harkokin dalibai.
Kwamred Musa Usman Sani ya bayyana hakan ne jim kadan bayan rantsar da sabbin shugabannin kungiyar ta dalibai ‘yan asalin jihar Kano NAKSS.
Ya ce, za su kawo sauyi wajen yiwa tsarin mulkin kungiyar ta NAKSS garambawul da kuma matsalolin da tsoffin shugabanni suka gaza kawo karshen su.
Da yake jawabi, sabon mai Magana da yawun kungiyar ta NAKSS a jami’ar Bayero, Kwamred Sulaiman Madobi, cewa yayi za suyi dukkan mai yiwuwa wajen ganin ana bai wa dalibai hakkin su tare da yin sabbin dokoki cikin tsarin shugabancin dalibai ‘yan asalin jihar Kano ta yadda za su gogayya da takwarorinsu na wasu jihohi.
An rantsar da shugabannin daliban a kujeru daban-daban har tsawon shekara daya.