Labarai
Kungiyar ECOWAS ta yi watsi da kalaman Trump na zargin kisan kiyashi ga Kiristoci a Najeriya

Kungiyar raya kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta yi watsi da zarge-zarge da shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya yi na ikrarin ana kisan kare dangi ga wani rukuni na addini a Najeriya
A wata sanarwa da ECOWAS ta fitar a daren Talata, kungiyar ta ce an yi amfani da irin waɗannan kalamai ne domin ɓata huldar ƙasashen yankin da kuma ƙara ta’azzara matsalolin tsaro.
Kungiyar ta tabbatar da cewa rahotanni masu zaman kansu sun nuna yadda ‘yan ta’addan ke kaiwa duk wanda suka ga dama hari, ba tare da wariyar addini ba.
ECOWAS ta jaddada cewa tashin hankalin da ake samu na da alaƙa da ta’addanci ne tsagwaronsa, kuma babu la’akari da bambancin jinsi, ko addini, ko kabila ko shekaru.
Sanarwar ta kuma yi kira ga duniya baki ɗaya da ta tsaya tare da ƙasashen yankin wajen yakar waɗannan ƙungiyoyin ta’addanci da ke zama barazana ga kowane al’umma.
Kungiyar ta nanata cewa ba za ta amince da waɗannan zarge-zargen masu haɗari wadanda ake amfani da su don ruguza zaman lafiya cikin al’umma da raunana haɗin kai ba, haka kuma akwai bukatar duniya ta tsaya tare da ƙasashen yammacin Afrika domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro.
You must be logged in to post a comment Login