Labarai
Kungiyar JOHESU ta fara aikin yajin aikin sai baba-ta-gani
Gamayyar Kungiyar ma’aikatar lafiya ta JOHESU, ta ce a daren jiya Talata ta fara yajin aikin sai baba-ta-gani a fadin kasar nan.
Shugaban kungiyar Josiah Biobelemoye ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja a jiya.
Biobelemoye ya kuma ce, tuni kungiyar ta umarci mambobinta da ke aiki a dukkannin Asibitocin kasar nan su tsunduma yajin aikin tare da kaucewa duk wani abu da ka iya kawowa kungiyar cikas a kan yajin aikin da ta fara.
Ya kuma kara da cewa ba za su janye yajin aikin ba har sai gwamnatin tarraya ta biya musu bukatunsu da su cimma yarjejeniya a kai, a ranar biyar ga watan Fabrairun da ya gabata.
Shugaban kungiyar Josiah Biobelemoye ya ce daga cikin bukatun na su akwai inganta albashin ma’aikata da samar da kayayyakin aiki Asibitocin gwamnatin.