Kiwon Lafiya
Kungiyar kididdiga ta kasa ta ce an shigo da tataccen mai sama da lita iliyan goma sha bakwai
Hukumar kididdiga ta kasa NBS ta ce kasar nan ta shigo da tataccen mai sama da lita biliyan goma sha bakwai a shekarar dubu biyu da sha bakwai da ta gabata.
Haka zalika ta kuma ce an shigo da man diesel lita biliyan ashirin da takwas a dai wannan wa’adin.
Hakan na kunshe ne cikin wani rahoto da hukumar ta fitar a jiya, wanda ya bayyana cewa a shekarar ta dubu biyu da sha bakwai an shigo da litar kalanzir sama da biliyan hudu.
A bangare guda kuma litar man jirgi da aka shigo da shi a shekarar ta kai sama da miliyan dari biyar da casa’in da biyu.
A cewar rahoton na NBS dai a watan Yuli da Ogusta ne aka shigo da litar man fetur mafi yawa, wanda a kowanne daya daga cikin watannin biyu aka shigo da lita biliyan daya da miliyan tamanin da takwas, yayin da kuma watanni Maris da Aprilu ne aka fi shigo da litar man diesel da kalanzir a cikin shekarar da ta gabata.