Labarai
Kungiyar Kiristoci CAN ta bukaci hadin kai tsakanin addinai

Kungiyar mabiya addinin Kirista ta kasa CAN ta bukaci ‘yan Najeriya da su rungumi hadin kai a tsakanin su
Ta cikin wani sako da ya aike a jawabinsa yayin bikin Easter na 2026. Shugaban kungiyar, Daniel Okoh, ya bayyana cewa Easter yana tunatar da mutane cewa duk wahala da ake ciki, akwai yiwuwar samun sauyi a cikin ta.
Kungiyar ta nuna damuwa kan halin da ‘yan kasa ke ciki sakamakon matsalolin tattalin arziki da rashin tsaro, wanda ya janyo damuwa.
Kazalika kungiyar ta bukaci shugabanni a dukkan matakai su nuna jagoranci mai ma’ana ta hanyar aiki a zahiri, tausayi, da kokarin inganta rayuwar jama’a.
Ta kuma jadda muhimmanci na hadin kai tsakanin addinai a kasar da samar da zaman lafiya mai dorewa
You must be logged in to post a comment Login