Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kungiyar kishin al’ummar Kano ta nesanta kanta da batun tsige sarki Sanusi na biyu

Published

on

Kungiyar kishin al’ummar Kano ta Kano Civil Society Forum ta musanta cewa ta aikewa fadar gwamnatin Kano bukatar a tsige sarki Muhammadu Sanusi na biyu daga mukaminsa.

Wannan na kunshe a wata wasika da kungiyar ta aikewa fadar gwamnatin Kano, tana mai cewa kungiyar Civil Society Organisation bata aike da wasikar bukatar a sauke Muhammadu Sanusi na biyu daga karagar mulki ba da yawunta ta yi hakan ba.

Kano Civil Forum dai ta kira waccan kungiyar da ta bukaci a sauke sarkin Kano daga mukaminsa a matsayin kungiya ta bogi.

Gwamna Ganduje ya nada Sarkin Kano Muhammad Sunusi shugaban majalisar Sarakunan Jihar Kano

Sarkin Kano zai fitar da mahaddatan alkur’ani karatu kasar waje

Kano: Abinda sa ya Ganduje ya zabi Sarki Sunusi II jagoran sarakuna

Kungiyar dai a cikin wasikar da ta aikewa gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta bayyana masa cewa akwai kungiyoyi masu zaman kansu sama da 183 da ke karkashinta da suka mayar da hankali wajen kare hakkin jama’a, harkokin kiwon lafiya, ayyukan raya kasa, harkokin tsaro da zaman lafiya.

Kano Civil Forum ta ta kuma yi Allah wadai da yadda wasu daidaiku ke amfani da siyasa wajen tayar da zaune tsaye, ta yadda suke fakewa da wata kungiya mai zaman kanta ta bogi.

Wasikar da kungiyar ta rubuta

“Muna mai nesanta kanmu daga wasikar da aka aikewa mai girma gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da ke neman a tsige sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu daga kan mukaminsa”, a cewar kungiyar.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!