Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Kungiyar kwadago ta bukaci a dau matakan Kariya na Corona

Published

on

Kungiyar kwadago ta kasa NLC, reshen jihar Kano ta bukaci ma’aikata gwamnati dasu kara himma wajen daukar matakan kariya na  yakar cutar Corona a fadin jiha da kasa baki daya.

Kiran  na cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar reshen jihar kano Kwamrade Kabiru Ado Minjibir.

Kwamrade Kabiru Ado Minjibir ya kuma bukaci al’umma dasu zauna a gidajen su, musamman ma ma’aikatan gwamnati na tsawon kwanaki goma sha hudu a wani bangare na dakile yaduwar cutar.

Labarai masu alaka.

A bi dokokin jami’an lafiya don kare yaduwar cutar Corona -Farfesa Musa Abdulkadir Tabari

Ganduje : za’a rufe kan iyakokin jihar Kano COVID-19

Haka zalika kungiyar ta bukaci masu ruwa da tsaki  da ma’aikatan lafiya da na  kafafen yada labarai dasu kara kaimi wajen fadakar da al’umma kan hanyoyin magance cutar mai lakabin Covid 19.

Har ila yau sanarwar ta kuma ja hankalin al’umma dasu cigaba da tsaftace muhallansu da wanke hannaye da kuma yin amfani da abun rufe fuska wato ‘FACE MASKS ‘ a matakan kiyaye kai daga kamuwa da cutar.

Sanarwar ta yabawa gwamnatin jihar Kano bisa daukar matakai daban -daban a fadin jiha a kokarin da take na dakile cutar Corona.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!