Kiwon Lafiya
Kungiyar kwadago ta bukaci gwamnati tarayya da tayi koyi da darasin zaben shugaban kasa na 1993
Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta bukaci gwamnatin tarayya da ta yi koyi da darasin da ke cikin zaben shugaban kasa na alif dari tara da casa’in da uku don dakile dukkannin matsaloli da za su kawo tarnaki ga gudanar da sahihin zabe a shekara mai zuwa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar Kwamared Ayuba Wabba.
Ta cikin sanarwar dai kungiyar ta NLC ta ce, ta yi hakan ne kungiyar kawai gwamnati za ta gamsar da al’ummar kasar nan cewa ta gamsu da sahihancin zaben da ake zato ya baiwa Chief MKO Abiola nasara.
Haka zalika Kwamared Ayuba Wabba a cikin sanarwar dai, ya kuma ce kamata ya yi gwamnati ta kara adadin mutanen da zata karrama musamman sanannu da sunansu suka yi shura wajen fafutukar ta June 12.