Labarai
Yajin aiki: Dalilan da suka sanya NLC ta yi watsi da umarnin kotu
Ƙungiyar kwadago ta Jihar Kano ta umarci mambobinta su tsunduma yajin aikin sai baba ta gani daga ranar litinin mai zuwa har sai sunji sanarwa daga ƙungiyar.
Shugaban ƙungiyar ta Kasa reshen Jihar Kano Kabiru Ado Mijibir ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan kammala tattaunawa da shugabanin ƙungiyoyin ƙwadagon a nan Kano.
Mijibir, ya ce, tafiya yajin aikin ya zama dole saboda yanayin da aka tsinci kai na tsadar rayuwa da kuma ƙarin farashin man fetur wanda hakan ya ƙara jefa rayuwar ma’aikata da masu ƙaramin karfi cikin mawuyacin hali.
Wakilinmu Abba Isah Muhammad, ya ruwaito shugaban ƙungiyar na kira ga sauran ƙungiyoyin da ɗaiɗaikun jama’a su bai wa ƙungiyar ƙwadagon hadin kai don samarwa jama’a mafita daga yanayin tsadar rayuwa da ake ciki.
You must be logged in to post a comment Login