Labarai
Kungiyar kwadago ta kasa ta ce batun dawowar tsarin mulkin demokradiya bai amfana komai ba
Kungiyar kwadago ta kasa NLC, ta ce tun bayan dawowar tsarin mulkin dimukuradiya a alif dari tara da casa’in da tara zuwa yanzu talakan kasar nan bai amfana da komai ba.
Shugaban kungiyar kwamared Ayuba Wabba ne ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa da sakatariyar kungiyar ta fitar, don ta ya al’ummar kasar nan murnar bikin ranar dimukuradiya ta bana, yana mai cewar, ‘yan siyasa ne kawai suke amfana da ita.
Ya ce ba a banza ba, aka kira sunan al’umma har sau uku a fassaran dimukuradiya, manufar hakan ita ce nuna cewa al’umma baki daya Yakamata su amfana da tsarin dimukuradiya ba wasu daidaiku ba.
Kwamared Ayuba Wabba ya kara da cewa, lokaci ya yi da al’ummar kasar nan zasu rika tambayar shugabanni kan alfanun da suka samu a mulkin dimukuradiya.
Shugaban kungiyar na NLC ta cikin sanarwar dai ya kuma jinjinawa ma’aikata wanda ya ce suke kan gaba wajen tabbatar da daurewar mulkin dimukuradiya.