Kiwon Lafiya
Kungiyar Likitoci reshen Jihar Ondo sun bayyana bukatun yajin aikin JOHESU da cewar hankali ba zai dauka ba
Kungiyar Likitoci ta kasa reshen Jihar Ondo NMA ta bayyana bukatun da kungiyar ma’aikatan Lafiya ta JOHESU a matsayin abinda hankali ba zai taba dauka ba kuma bai dace da tsarin kasashen Duniya ba.
Kungiyar ta NMA ta ce yajin aikin JOHESUN wanda ya janyo tabarbarewar harkokin kiwon lafiya a fadin kasar nan, kwata-kwata bai dace ba, duba da halin tagayyara da marasa lafiya suka shiga.
Wannan kuma na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar Likitocin shiyyar Jihar Ogun ta yi tir da umarnin JOHESUN ta baiwa mambobinta na Jihohi da kananan hukumomi su ma su tsunduma yajin aikin.
Shugaban kungiyar ta NMA reshen Jihar ta Ondo Dokta Zacharia Gbelela ke cewa al’ummar kasar nan na nuna rashin jin dadinsu da wannan yajin aiki, kuma babu wata kasa a Duniya da ake biyan albashin Likitoci daidai da na ma’aikatan lafiya.
Sannan ya shawarci kungiyar JOHESU ta sake tunani kan wannam taki da ta dauka na tsunduma yajin aiki da ya yi sanadiyyar jefa al’ummar kasa cikin halin ni ‘ya-su.