Labarai
Kungiyar ma’aikatan lafiya ta JOHESU a Najeriya ta tsunduma yajin aiki

Hadaddiyar Kungiyar Ma’aikatan Lafiya JOHESU da Kungiyar Kwararru a Fannin Kiwon Lafiya a Najeriya sun fara yajin aiki a yau Asabar.
Kungiyoyin sun ce gazawar gwamnatin kasar wajen aiwatar da sabon tsarin albashin ma’aikatan lafiya da kuma kawo karshen matsalolin da suka jima suna korafi a kan su ne musabbabin tafiya yajin aikin.
Bayanin hakan na kunshe ne a wata sanarwa da shugaban JOHESU na Kasa, Kwamared Kabiru Ado Minjibir, ya sanayawa hannu.
Yajin aikin na kungiyoyin na zuwa ne a daidai lokacin Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta kasa ta ke nata yajin aikin saboda rashin biyan wasu bukatunta.
Ana fargabar yajin aikin da kungiyoyin ke yi zai durkusar da harkar kiwon kafiya a asibitocin gwamnatin tarayya da na jihohi da dama a fadin Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login