Kiwon Lafiya
Kungiyar malamai jami’oi ta shiga sati na bakwai a yajin aiki
Kungiyar malaman jami’o’I ta kasa ASUU ta ce yajin aikin da da take yi a yanzu da ya shiga sati na bakwai, sun tsundumane saboda girmama bukatun bukatun kasa.
Shugaban kungiyar ta ASUU Farfesa Biodun Ogunyemi ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai, a wani bangare na maida martani kan kiraye-kirayen da ake yi na su janye yajin aikin.
A cewar sa ba za su janye yajin aikin ba domin kuwa suna yi ne domin ra’ayin al’ummar kasa da kuma girmama bukatun al’umma.
Ya kara da cewa ba za su janye yajin aikin ba har sai gwamnatin tarayya ta cika dukkanin bukatun da malaman jami’ar da kuma jami’o’in ke bin gwamnatin.
Batun bukatar janye yajin aikin ya fara tsananta ne tun a lokacin da hukumar zaben ta kasa INEC ta furta cewa yajin aikin ka iya kawo tarnaki kan zaben wannan shekara.
Ana sa ran cewa kungiyar ta ASUU da kuma hukumar zaben ta kasa INEC zasu gana a ranar juma’a mai zuwa domin lalubo bakin zaren.