Labarai
Ma’aikatan lantarki sun koma bakin aiki
Kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa NUEE, ta janye yajin aikin sai baba ta gani da ta fara a jiya Laraba da nufin janyo hankalin gwamnatin tarayyar Najeriya kan hakkokin mambobinta.
Kungiyar dai ta sanar da janye yajin aikin ne da safiyar yau alhamis sakamakon wani zaman gaggawa da ta yi da jami’an gwamnatin tarayya.
Shugaban kungiyar ta NUEE na kasa kwamared Joe Ajaero ne ya tabbatar da janye yajin aikin ga manema labarai, yana mai cewa, sun tattauna matsalolin ma’aikatan sosai kuma gwamnatin tarayya ta yi alkawarin shawo kan matsalar.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, shiga yajin aikin kungiyar ya biyo bayan karewar wa’adin kwanaki 21 da ku kungiyar ta baiwa ministan lantarki Saleh Mamman, domin duba bukatun mambobinta, inda kuma rashin sauraron su da ya yi ne ya sanya su fara yajin aikin.