Labarai
Kungiyar manoman shinkafa RIFAN ta dakatar da shirin ba da rance a Kano
Kungiyar manoman shinkafa ta kasa RIFAN ta dakatar da shirin ba da rance ga manoma na Ancho borrowers a nan Kano nan take ba tare da bata lokaci ba.
Shugaban kungiyar reshen jihar Kano Alhaji Abubakar Haruna Aliyu ne ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai.
Ya ce, dakatar da shirin na ancho borrowers zai taimaka wajen gudanar da cikakken bincike kan zargin da hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ke yi kan shugabannin kungiyar ta RIFAN.
Alhaji Abubakar Haruna Aliyu ya kuma ce kungiyar tana alhinin sanar da dukkan nin mambobinta cewa daga yanzu, an dakatar da gudanar da shirin na ancho borrowers a nan Kano zuwa wani lokaci.
Ya kara da cewa uwar kungiyar ta kasa ce ta ba da umarnin dakatar da shirin anan Kano don bai wa hukumomi dama da su gudanar da bincike game da zargin almundahana.
Shirin ancho borrowers dai shiri ne na gwamnatin tarayya da aka kirkiro da nufin bai wa manoma bashi ta hannun babban bankin kasa CBN.
You must be logged in to post a comment Login