Kiwon Lafiya
Kungiyar manyan dillalan man fetur DAPPMA ta janye yajin aikin da zata fara a yau
Kungiyar manayan dillalan man fetur ta Najeriya DAPPMA ta janyi umarnin da ta bayar na rufe dukkanin depo-depo da ake dakon mai a fadin kasar nan da zai fara aiki daga sha biyun daren yau litinin, inda ta sake ba da wa adin kwanaki biyar ga gwamnti ta sake bibiyar lamarin.
Umarnin dakatarwar ya fito ne ta cikin wata sanarwa da sakataren kungiyar ta DAPPMA Olufemi Adewole ya fitar da tsakar daren jiya Lahadi a jihar Lagos.
Ta cikin sanarwar Olufemi ya ce a baya kingiyar ta baiwa dukkanin mambobin ta umarni rufe depo-deopn biyo bayan dumbin basukan da suke bin gwamnati tarayya da kuma har yanzu ta gaza biyan su amma a yanzu ta yi sassauci.
Sanarwar ta kara da cewa biyo bayan sanya bakin wasu masu fada aji a kasar nan musamman ma kwamitin majalisar dattijai kan albarkatun man fetur, ya sanya kungiyar da janye daga umarnin, ta kuma sake baiwa gwamanti wa’adin kwanaki biyar su magance matsalar.
Ya kuma ce kungiyar ta dauki matakin janyewar ne la’akari da irin halin da al’ummar kasar nan za su shiga matukar suka tafi yajin aikin musamman ma a wannan lokaci na karshen shekara.