Kiwon Lafiya
Kungiyar manyan malaman jami’o’i ta kasa ASUU sun daidata da gwamnatin tarayya
Kungiyar manyan malaman jami’o’I ta kasa ASUU ta dai-daita da gwamnantin tarayya a jiya litinin don ganin an kawo karshen yajin aikin da aka kwashe tsahon lokaci ana gudanarwa.
Sanata Chris Ngige wanda shine Ministan kwadago, ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala taron tattaunawar da aka gudanar tsakanin su da kungiyar ta ASUU.
Ngige ya kuma ce an samu abin da ake bukata na kyakyawar matsaya a yayin gudanar da taron, inda ya ce gwamnantin tarayya ta ware naira biliyan 15 da miliyan 4 don biyan kudaden albashi wanda yana cikin manyan bukatun malaman.
Sannan ya ce gwamnati zata ci gaba da duba manyan bukatun su da kuma duba yiwuwar biya musu cikin dan kankanin lokaci.
Da ya ke jawabi shugaban kungiyar na kasa Farfesa Biodun Ogunyemi ya ce kwamitin gudanarwar kungiyar zai sake zama don yin duba kan bukatun nasu wanda zai yi dai-dai da matsayar da aka cimma da gwamnantin tarayya.
Sannan ya ce za’a janye yajin aikin ne idan kwamitin gudanarwar kungiyar ya kammala zaman sa, sai dai bai fadi lokacin da kwamitin zai zauna ba.
Malaman jami’a dai sun tsunduma yajin aiki ne tun ranar 4 ga watan Nuwambar shekarar bara kan abinda suka kira rashin cika musu alkawurran da gwamnantin tarayya ta daukar musu a yajejeniyar da su sha kullawa.