Labarai
Kotu ta hana Abba Gida-gida rushe gine-ginen BUK Road
Kungiyar mamallaka gine-gine da ke kan titin tsohuwar jami’ar Bayero ta Kano, sun bukaci gwamnatin jihar da ta yi biyayya ga umarnin da kotu ta yi na dakatar da rushe gine-ginensu kasancewar sun mallaki filayensu bisa ka’ida.
Guda cikin masu gine-ginen Alhaji Sani Mustapha Kurmawa, ne ya bukaci hakan yau Alhamis yayin taron manema labarai da kungiyar ta gudanar domin ankarar da gwamnati kan dakatar da rushe gine-ginen da ke kan titin na tsohuwar jami’ar Bayero.
Alhaji Sani Mustapha Kurmawa, ya kuma ce, “yanzu haka mun shiga kotu, kuma ta bayar da takardar dakatar da gwamnati bisa yunkurinta na rushe mana gine-gine”.
“A cewar gwamnati filayenmu na kan badala, don haka aka sanya Jan Fenti tare da ba da umarnin rushe mana gine-gine”.
Sai dai kuma a fadar sa ‘ba su ne suka fara gini akan badala ba, gwamnatin can baya ma tayi hakan dan haka bai kamata ace lokaci daya azo ace musu sunyi gine ba akan yadda ya dace ba’.
A shekaran jiya Talata ne Babbar kotun jiha da ke kan titin Miller Road a birnin Kano ta dakatar da gwamnantin Kano daga yin rusau a gine-ginen da ke jikin Badala a kan titin na zuwa jami’ar Bayero.
Kotun, ta bayar da umarnin ne bayan da mamallaka wuraren suka roki da ta duba halin da suke ciki, la’akari da cewar bisa ka’ida suka mallaki wuraren.
Mai shari’a Hafsat Yahya Sani, ce ta bayar da umarnin dakatarwar har sai kotu ta nazarci al’amarin.
Haka kuma ta sanya ranar 26 ga Oktoba mai zuwa a matsayin ranar da za a saurari shari’ar.
Rahoton: Umar Abdullahi Sheka
You must be logged in to post a comment Login