Kiwon Lafiya
Kungiyar mawakan jihar kano ta ce akwai bukatar koyi da mawakan da suka gabata
Kungiyar Mawaka ta kasa reshan Jihar Kano ta bayyana cewar kamata ya yi mawakan wannan zamani su yi koyi da tsarin wakokin mawakan da suka gabata wajen inganta wakokinsu, don ci gaban al’umma.
Shugaban Kungiyar Malam Khalid Imam ne ya bayyana hakan a yau jim kadan bayan kammala Shirin Barka da Hantsi na nan gidan Rediyo Freedom.
Khalid Imam ya kara da cewar wasu daga cikin mawakan wannan zamani ba su da yin wakokin Fadakarwa ko jan hankali ba domin kawo gyara cikin al’amuran jama’a na yau da kullum.
Malam Kahlid Imam ya yi kira ga mawakan su kasance masu bada gudumawa ga ci gaban matasan mawaka masu tasowa.
Shugaban Kungiyar ya kuma yi kira gwamnati da ta rinka tallafawan musamman ma wajen bada shawara a harkokinsu na rubuce-rubucen wakokin don ci gaban al’umma ba wai sai lallai na siyasa ba.