Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Kungiyar mawakan jihar kano ta ce akwai bukatar koyi da mawakan da suka gabata

Published

on

Kungiyar Mawaka ta kasa reshan Jihar Kano ta bayyana cewar kamata ya yi mawakan wannan zamani su yi koyi da tsarin wakokin mawakan da suka gabata wajen inganta wakokinsu, don ci gaban al’umma.

Shugaban Kungiyar Malam Khalid Imam ne ya bayyana hakan a yau jim kadan bayan kammala Shirin Barka da Hantsi na nan gidan Rediyo Freedom.

Khalid Imam ya kara da cewar wasu daga cikin mawakan wannan zamani ba su da yin wakokin Fadakarwa ko jan hankali ba domin kawo gyara cikin al’amuran jama’a na yau da kullum.

Malam Kahlid Imam ya yi kira ga mawakan su kasance masu bada gudumawa ga ci gaban matasan mawaka masu tasowa.

Shugaban  Kungiyar ya kuma yi kira gwamnati da ta rinka tallafawan musamman ma wajen bada shawara a harkokinsu na rubuce-rubucen wakokin don ci gaban al’umma ba wai sai lallai na siyasa ba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!