Labarai
Kungiyar Miyetti Allah ta ce akwai bukatar kula da shige da ficen makiyaya
Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ta bukaci gwamnatin tarayya da ta rika kula da shige da ficen makiyaya a kan iyakokin kasar nan.
Sakataren kungiyar na kasa Alhaji Baba Ngelzarma ne ya yi wannan kiran yayin wani taron manema labarai jiya a Abuja.
A cewar sa ya zama wajibi gwamnati ta kula da kan iyakokin kasar nan domin kula da makiyaya bakin haure da ke shigowa cikin kasar nan.
Ya ce kodayake akwai yarjejeniyar shige da fice tsakanin kasashen yammacin afurka ta Ecowas amma hakan ba zai hana gwamnati kula da zirga-zirgar makiyaya akan iyakokin kasar nan ba, inda har ya buga misali da Jamhuriyar Nijar wanda ya ce ta dau matakin kula da zirga-zirgar makiyayanta.
Alhaji Baba Ngelzarma ya kuma bukaci da a biya mambobinta wadanda suka rasa rayukansu da wadanda suka rasa kadarorinsu diyya.
A cewar Kungiyar ta MACBAN a Mambilan jihar Taraba ka dai mambobinta dari bakwai da talatin da biyu ne suka rasa rayukansu, yayin da a kashe wasu tamanin da biyu a Numan din jihar Adamawa cikin su kuwa har da mata da kananan yara.
Sakataren kungiyar na Miyetti Allah ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sake sabunta tsarin nan na ware kebabbun wuraren kiwo ga makiyaya wato Grazing reserves maimakon sabon tsarin da gwamnati ke son bullo da shi wato cattle colonies.