Kiwon Lafiya
Kungiyar NANS ta baiwa gwamnatin tarayya da kungiyoyin jami’oi ta ASUU wa’adin makwannin biyu
Kungiyar dalibai ta kasa NANS ta bai gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’I ta kasa ASUU wa’adin makwanni biyu da su daidaita tsakanin su, ko ta kalubalance su.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar Danielson Akpan, da ya fitar da yammacin jiya aka rabawa manema labarai.
Ta cikin sanarwar kungiyar ta NANS ta ce bayan koma bayan da ake ta samu a tattaunawar gwamnatin da malaman jami’ar, ta ga dacewar tabada wa’adin makwanni biyun su sasanta, ko kuma ta kalubalnce su.
Tun dai a ranar 4 ga watan nuwambar da ya gabata ne kungiyar malam jami’o’I ta kasa ASUU ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani bisa abinda ta kira gazawar gwamanti wajen biyan bukatun su.
Haka kuma kungiyar ta gudanar da zaman tattaunawa da dama da bangaren gwamanti amma har yanzu ba a akai ga cimma matsaya a tsakanin sub a.