Kiwon Lafiya
Kungiyar NUPENG ta bayyana rashin jin dadinta kudaden da ake zargin an rage a kasafin kudin bana
Kungiyar ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas NUPENG ta rashin jin dadinta, kan kudaden da ake zargin ‘yan-Majalisar tarayyar kasar nan sun rage daga cikin kasafin kudin bana, musamman abinda ya shafi bangaren ayyukan gina manyan tituna.
Shugaban kungiyar William Akporeha ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a jiya Lahadi, yana mai cewa zaftare kudin manyan ayyukan ka iya kawo koma-baya cikin farfadowar da kasar nan ke yi daga masassarar tattalin arziki.
A larabar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zargi Majalisun tarayyar kasar nan da zaftare wani bangare na kasafin kudin bana da ya aike musu da shi domin tantancewa, inda kuma suka yi cushen wasu ayyuka na kashin kansu da basu da muhimmanci sosai.
Daga cikin ayyukan da kwaskwarimar ta shafa sun hadar da na Titin Badin zuwa Shagamu zuwa Lagos, da aka ware Naira biliyan 11 da miliyan 500, inda aka zaftare Naira biliyan 1 da miliyan 14 daga ciki.
NUPENG din ta bayyana tituna a matsayin wani bangare da ke taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.
Har ila yau kungiyar ta shaida cewa rashin kyawun titunan na janyo hatsari da ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi