Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Kungiyar SERAP ta bukaci shugaba Buhari da ya kalli rahoton cin hanci da rashawa

Published

on

Kungiyar tabbatar da dai-daito a ayyukan gwamnati SERAP ta bukaci gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da ta kalli rahotan da kungiyar Transparency International ta yi fitar kan ma’aunin cin hanci da rashawa a Najeriya na kwana-kwanan da kyakyawan niyya.

 

Kungiyar ta SERAP ta ce mai makon gwamnatin tarayya ta yi watsi da rahoton kamata ta yi ta karba da hannu biyu-biyu wajen sake yin dammara da yaki da cin hancin da rashawa.

 

Wannan na dauke cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan kungiyar Timothy Adewale ya fitar a karshen makon da ya gabata cewa gwamnatin tarayya ta dauki rahoton da muhimmanci kuma ta yi amfani da shi amatsayin wata dama na kara kaimi wajen yaki da cin hanci da rashawa.

 

A dai rahotan ta na kwan-kwana nan da Kungiyar Transparency International ta fitar, ta sanya Najeriya a matsayin lamba na 148 daga cikin kasashe 180 a duniya, tana mai cewar cin hanci da rashawa yayi kamari a Najeriya a cikin shekaru 2 da suka gabata bayan da ta sanya ta a cikin jerin kasashe 136 a ‘yan shekarun da suka gabata.

 

Sai dai fadar shugaban kasa ta yi watsai da rahotan na kungiyar Transparency International kan cin hanci da rashawa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!