Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Gwamnatin tarayya zata baiwa manoman audiga fiye da 100 tallafi

Published

on

Gwamnatin tarayya zata baiwa manoman Audiga fiye da dubu dari 100 tallafin bunkasa harkokin  noman su karkashin shirin babban bankin nageriya a wannan shekarar ta 2019.

Karamar ministan ciniki da masanaantu Hajiya Aisha Abubakar ta bayyana haka a jiya laraba a Zariya ,yayin taron bitar yini guda da akayi domin samar da irin audiga da zai bunkasa noma a jihar Niger.

Taken taron bitar shine yadda za’a kara farfado da irin noman audiga  mai inganci audiga domin bunkasa masanaatun kasar nan da suke sarrafa tufafi.

Karamin ministan ta samu wakilcin madam Omolulu Opeewe wadda darakta ce a ma’aikatar tace gwamnatin tarayya ta bawa tsarin noman audiga fifiko domin inganta noman sa a kasar nan.

Tace ci gaba da cewa, tsarin farfado da tatalin arziki yasa gwamnatin tarayya  kokarin inganta noman audiga Najeriya

Ta kara da cewa,dalilin fito da shirin dan kara wa manoman cikin gida kwarin gwiwa dan bunkasa noman audiga .

Ministar ta kara da cewa,domin tabatta da tsarin shi yasa maaikatar tashigo da maaikatu da hukumomin gwamnati da masu ruwa da tsaki domin fito da sababbin hanyoyin zamani dan inganta noman audiga.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!