Siyasa
Jam’iyyun adawa sun bukaci INEC ta tsawaita wa’adin da ta bayar na zaben fidda gwani

Jam’iyyun adawa a kasar nan sun bukaci Hukumar Zabe ta Kasa INEC da ta tsawaita wa’adin ta ta bayar na gudanar da zaben fidda gwani domin zaben 2027 zuwa karshen watan Yuli, 2026.
Sun bayyana hakan ne a taron kasa da suka gudanar a Ibadan, da ke Jihar Oyo, inda suka ce wa’adin da aka saka na ranar 30 ga Mayu bai zai wadatar da su ba.
Jam’iyyun da suka hada da ADC, PDP da NNPP sun ce karin lokaci zai ba su damar shirya sahihin zaben fidda gwani tare da samar da daidaito tsakanin dukkan jam’iyyu kafin babban zaben 2027.
Bugu da kari, jam’iyyun sun bayyana rashin amincewa da shugaban INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan, bayan da suka zargeshi da nuna son kai da bangaranci ga APC.
Haka kuma sun bukaci Majalisar Dokoki ta sake duba dokar zabe ta 2026 tare da neman a sako wasu ‘yan siyasa da suka ce ana tsare da su kan laifukan da za a iya bayar da beli.
You must be logged in to post a comment Login