Labarai
Kungiyar tagwaye na yaki da barace-barace tare da ‘yan biyu a Kano
Kungiyar ‘yan tagwaye ta kasa dake nan jahar Kano wacce ake kira da Tagwe forum ta sha alwashin kawo karshen barace-barace da wasu iyayen ‘yan biyun ke yi da su a titinan kasar nan saboda rashin karfi yadda zasu kula da su.
Shugaban kungiya injiniya Hassan Ahmad Makari ne ya bayyana hakan ya yin ziyarar kulla alaka da suka kawo nan tashar Freedom Radiyo a yau Talata.
Inginiya Hassan Ahmad ya ce sun kafa kungiyar ne a kokarinsu na ganin sun samar da ingantattaciyar rayuwa a tsakanin su musamman ta bangarorin karatu da sana’a da kuma auratayya.
Da yake jawabi shugaban tashar Freedom Radiyo Kano Malam Ado Sa’idu Warawa ya ce Freedom Radiyo zata baiwa kungiyar ta Tagwaye gudunmaw a wajan ganin sun ciyar da al’umma gaba.
Wakiliyar mu Aisha Shehu Kabara ta ruwaito cewar kungiyar ta ‘yan Tagwaye tayi kira ga iyayen yaran da basu da karfin kula da yaran da su nemi kungiyar domin tallafa musu.
You must be logged in to post a comment Login