Labaran Kano
Kungiyar ‘yan tifa ta musanta rashin birkin motocinta
Kungiyar Direbobin Tifa ta kasa reshen jihar Kano ta ce ko wace motar tifa dake dibar yashi a Kano tanada cikakken burki, ba kamar yadda wasu ke zargin babu ba.
Kungiyar tace yawaitar korafin samu afkuwar hadura a inda direbobin motar ya rutsa dasu ko kuma makamancin haka a fadin jiha ya jawo yawaitar cecekuce akan motocin da direbobin su.
Hakan ya sa al’umma da dama ke zargin cewa rashin birki ke haddasa samun hadura a titunan jihar Kano.
Shugaban kungiyar direbobin Tiffofi ta kasa reshen jihar Kano Kwamred Mamuni Ibrahim Takai, ne ya tabbatar da hakan lokacin bude bita ga direbobin tifar yashi na Kano wanda kungiyar ta shirya da hadin gwiwar hukumar lura da ababen hawa VIO reshen jihar Kano da kuma Ma’aikatar gidaje da sufuri ta Kano.
labarai masu alaka.
Ana zargin KAROTA da haddasa hatsari a titin Zariya
Mamuni Ibrahim, ya ce gudun wuce sa’a da wasu direbobin tifar ke yi ke haddasa hatsarin da ke sa ba’a iya shawo kan tifar da wuri da hakan ke saka shakku a zukatan al’umma cewar motocin basu da birki.
Mamuni Ibrahim, ya tabbatar da cewa a halin yanzu mafi yawa daga cikin direbobin Tifofin na amfani ne da sabbin motoci na zamani.
You must be logged in to post a comment Login