ilimi
Kungiyoyin kishin al’umma su rinka tallafawa fannin Ilimi-Sarkin Kano
Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci kungiyoyin kishin al’umma da su rika tallafawa wajen ciyar da harkokin Ilimi gaba a kasar nan.
Shugaban majalisar sarakunan Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana hakan a Laraba 27 ga watan Oktobar 2021 lokacin da cibiyar Zam-Zam alkairi ta kai masa ziyara fadar sa domin shaida masa irin ayyukan da suke yi don sanya albarka.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya kuma ce idan kungiyoyi na taimakawa fannin ilimi a kasar nan ba za’a fuskanci matsaloli da ake samu ba a fannin.
A nasa jawabin shugaban cibiyar Zam-Zam alkairi Dakta Ibrahim Abdullahi Rijiyar Lemo, ya godewa sarkin na Kano bisa irin kokarin da yake wajen ciyar da ilimi gaba da al’ummar jihar Kano baki daya.
Mai martaba sarkin na Kano ya karbi ayarin shuwagabanin makarantar koyar da kiwon lafiya a Kano ta Aminu Dabo College of Health Science a fadar sa yau.
You must be logged in to post a comment Login