Labaran Wasanni
Kuri’ar Yankan Kauna : An kusan tsige shugaban Barcelona
Kuri’u 271 suka rage kafin a yi nasara a yunkurin kada kuri’ar yankan kauna ga shugaban kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Josep Maria Bartomeu.
Rahotanni na cewa, wani daga cikin rukunin kungiyar mai suna ‘Mes que una Mocio’ ne suka kirkiro zaben kada kuri’ar yankan kauna ga shugaban.
Runkunin ya ce, kawo yanzu sun samu kuri’u dubu 16,250, inda ya rage saura kuri’u 271 cikin kuri’u dubu 16,521 da ake bukata don tsige Josep Maria Bartomeu daga shugabancin kungiyar.
Haka kuma, a yau Alhamis ne ake dakon kammala kada kuri’ar domin mika wa kungiyar ta Barcelona a filin wasa na Camp Nou.
You must be logged in to post a comment Login