Kiwon Lafiya
Kwamitin da ke binciken zargin fitar da biliyan 33 daga asusun hukumar kula da fansho zai gabatar da rahoton sa
Kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai da ke binciken zargin fitar da naira biliyan talatin da uku daga asusun hukumar kula da fansho ta kasa zai gabatar da sakamakon rahoton sa a makon gobe.
Shugaban kwamnitin Benjemin Wayo ne ya bayyana hakan jiya Alhamis yayin zantawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja.
Ya ce burin kwamitin shi ne kawo gyara a harkokin fanshon Najeriya, a don haka ta yi cikakken bincike domin gano gaskiyar lamarin.
Haka haka masu binciken sun bukaci masu ruwa da tsaki da al’ummar Najeriya nan da cewa, idan suna da wani bayani da zai taimakawa kwamitin kan hukumar ta ‘yan fansho ta kasa da su rubuta wa kwamitin nan da kwanaki hudu masu zuwa.
Ya kuma ce kwamitin zai shawarci gwamnati da ta karbi bayanan da al’umma suka shigar gaban ta saboda hakan zai taimaka wajen binciken.