Labarai
Kwamitin daukar ma’aikata na Kano zai magance yin kutse – Abubakar General
Kwamitin daukan ma’aikata a kananan hukumomin jihar Kano wanda gwamnatin tarayya zata yi da ya kai dubu dari bakwai da saba’in da hudu a jihohin kasar nan 36, ya ce zai mangance yin kutse a shirin samar da aiki yi da za’a yi nan bada jimawa ba.
Sakataren yada labarai na kwamitin daukar ma’aikata na jihar Kano Abubakar Muhammad general ne ya bayyana hakan a yau, jim kadan bayan kammala shirin “Barka da Hantsi” na nan tashar freedom radiyo, wanda ya maida hankali kan yadda tsarin daukan matasan aiki zai kasance a jihar Kano.
A cewar general, kwamitin a nan Kano mai dauke da mutum Ashirin ya tsara rarraba form din shaidar samun gurbin aikin ga matasa don magance samun masu yin kutse a irin wannan sha’ani.
Abubakar Muhammad ya kuma ce, za a fara shirin ne a ranar daya ga watan Okotoba, kuma zai dauki tsawon watanni uku ana yin sa tare da biyan ma’aikata dubu Ashirin a kowanne karshen wata.
General Abubakar ya ce, kwamitin ya hada da sarakunan gargajiya da malamai da sauran masu fada aji, a don haka akwai bukatar al’ummar jihar Kano musamman wadanda suke da aiki su bai wa marasa aikin yi damar samun shiga shirin don magance matsalolin matasa marasa aikin yi a kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login