Labarai
Gwamnatin Kano za ta tilastawa kamfanoni masu zaman kansu bai wa al’ummar jihar ayyukan yi

Kwamitin tabbatar da daidaito na rabon guraben aiki ga al’ummar jihar Kano ya ce nan gaba kadan dokar da za ta tilastawa kamfanoni masu zaman kansu bawa al’ummar jihar nan guraben aiki za ta fara aiki.
Shugaban kwamitin Dakta Ibrahim Garba Muhammad ne ya bayyana halin da ake ciki kan aikin da kwamitin ya sanya a gaba.
Yace yanzu haka ana kokari a fito da wani jadawali wanda zai tabbatar da cewa dukkanin wata ma’aikata da za ta shigo jihar Kano ta gudanar da kasuwanci dole ne ta bada gurbin aiki ga al’ummar Kano.
Dakta Ibrahim Garba Muhammad nan bada jimawa ba za’a fito da dokar kuma za ta fara aiki a dukkanin ma’ikatu da kamfanoni masu zaman kansu.
You must be logged in to post a comment Login