Connect with us

Labarai

Kwana ɗaya da rushe SARS: Ƴan fashi sun kai hari a Kano

Published

on

Wasu mahara sun kai hari rukunin shagunan Shy Plaza da ke unguwar Ƙofar Gadon Ƙaya a birnin Kano.

Lamarin ya faru ne bayan ƙarfe bakwai na daren yau Talata.

Wani shaidar gani da ido ya shaida wa Freedom Radio cewa, ƴan fashin sun zo ne su huɗu a mota ɗauke da bindigu inda suka riƙa harbin iska a sama.

Daga nan ne kuma mutane suka shiga gudu, su kuma suka shiga wasu shaguna biyu na sayar da kwamfiyuta da kuma shagon hada-hadar kuɗi na POS suka yi awon gaba da kayayyaki.

Ɗaya daga cikin masu shagunan da lamarin ya shafa Musaddiƙ Sidi Bala ya shaida wa Freedom Radio cewa, ƴan fashin sun yi awon gaba da kwamfiyutoci na kimanin naira miliyan ɗaya da dubu arba’in da biyar, baya ga wayoyin hannu da kuɗaɗe.

Har kawo yanzu hukumomin tsaro a Kano ba su ce komai ba kan faruwar lamarin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!