Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kwankwaso ya amince a karɓi Ado Doguwa a NNPP

Published

on

Ɗan Takarar Shugaban ƙasa a jam’iyyar NNPP Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce a shirye yake ya karɓi shugaban masu rinjaye na majalisar tarayya Alhassan Ado Doguwa.

Jigo a jam’iyyar NNPP kuma ɗan takarar majalisar tarayya a ƙananan hukumomin Rano Kibiya da Bunkure, Kabiru Alhassan Rurum ne ya bayyana hakan.

Ya ce, hakan ya biyo bayan iƙrarin da Doguwa yayi na cewar Kwankwaso bai yi masa ta’aziyya ba.

Yanzu haka Kwankwaso ya kafa Kwamitin mutane huɗu ƙarƙashin jagorancin Sanata Rufa’i Sani Hanga da Rt. Hon Kabir Alhassan Rurum da shugaban NNPP na Kano Hon. Umar Haruna Doguwa da kuma Hon. Sarki Aliyu Danjeji domin su je su yiwa Ado Doguwa gaisuwa a madadin Kwankwason.

Rurum ya ce, siyasa harka ce ta jama’a, kuma babu masoyi ko maƙiyi na dindin.

Meye ra’ayinku a kai?

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!