Labarai
Kwankwaso ya zargi gwamnatin tarayya da gaza magance matsalar tsaro

Tsohon Gwamnan Kano kuma dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, a zaben shekarar 2023 , Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya soki gwamnatin tarayya, da cewa ta gaza wajen magance matsalar tsaro da ke ƙara yaduwa a faɗin Najeriya.
Ta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sanata Kwankwaso ya ce, yadda gwamnati ta bar jihohi su kafa ƙungiyoyin sa-kai ba tare da horo na musamman ba, ya kara tabarbara tsaron kasar da ya jawo yawaitar kananan makamai a hannun batagari da rura wutar rikice-rikice.
Haka kuma, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana takaicin sa kan wariya da rarrabuwar kai da ƙabilanci da tsangwama da cin zarafi da ke faruwa a wasu yankunan Najeriya tare da yawaitar kalaman ƙiyayya a kafafen sada zumunta.
You must be logged in to post a comment Login