Labaran Wasanni
Kwantiragin Messi ya kammala a Barcelona
Shahararran dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Lionel Messi, yanzu haka ya zama dan wasan da bai da wakili a hukumance.
Yanzu haka dai kwantiragin Messi da Barcelona ya kare, bayan yunkurin da ya gaza kaiwa ga ci na ficewa daga kungiyar watanni 12 baya.
Yarjejeniyar da shahararren dan wasan na kasar Ajantina ta kare ne a tsakar dare jiya Laraba 30 ga watan Yunin 2021, inda ake jita-jitar cewa dan wasan ya gaza yin karin wa’adi kwantiragin.
Haka zalika, Barcelona tana gudanar da tattaunawa da wakilin Messi kan batun sabunta kwantiragin don ci gaba da zama a kungiyar.
You must be logged in to post a comment Login