Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Kwara ta lallasa jihar Bauchi a gasar Ramat Cup

Published

on

An kammala gasar cin kofin Kwallon kafa ta matasa ‘yan kasa da shekaru 16, na kasa, mai taken Ramat Cup, na tunawa da tsohon shugaban kasa mulkin Soja, marigayi Murtala Muhammad yammacin jiya jumu’a a nan Kano.

Wasan wanda shi ne karo na 37, an fafata tsakanin jihar Bauchi da Kwara, inda jihar Kwara ta samu nasara da ci daya da nema bisa jihar Bauchi a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata.

Jihohi 20 ne dai suka shiga gasar ta bana, wadda aka karkare a yau da nasarar jihar ta Kwara, wacce ita ke rike da kambu, na kofin bayan nasarar data samu a shekarar 2018 kasancewar ba a gudanar da gasar ba a shekarar 2019.

Hotuna daga wurin taron rufe gasar:

Da yake jawabi a wajen rufe gasar shugaban wasannin matasa na kasa wato Youth Sport Federation of Nigeria (Ysfon), kuma mataimakin gwamnan jihar Kano Alhaji Nasiru Yusif Gawuna, yace hukumomi a matakai daban-daban, zasu cigaba da tallafawa wasannin matasa kasancewar wasa shi ne tushen da yake hada kan al’ummar kasar nan a gefe daya kuma, ya samar musu da sana’a.

Tun da fari dai, an buga wasan neman na uku, inda jihar Rivers ta samu galaba akan jihar Kogi da ci daya da nema.

Kafin daga bisani jihar Kwara ta samu galaba akan jihar Bauchi da Kwallo daya tilo da Abubakar Usman, ya zura a mintuna 15 din farkon rabin lokaci, daya daga ciki ‘yan wasan jihar ta Kwara Bashir Sharif, ya bayyana jin dadin sa da yadda jihar sa tayi galaba a wasan.

Har ila yau a gasar, an yi gudun tserere na mita 200, inda dan wasa Josiah Joel daga Kaduna ya kare a mataki na farko a sakan 22, Al’amin Usman daga jihar Kano ya yi na biyu a sakan 23, sai Adaralegba Temitope, daga jihar Ekiti da ya karkare a mataki na uku da sakan 24.

Sai gudun mita 100, na yan wasa hudu (04), da jihar Kano tayi na daya ta hannun dan wasa Abubakar Alhassan, da sakan 46 da digo 40, ya yinda Alex daga Kwara ya kare a mataki na biyu da sakan 46, da digo 52, sai Adamu Jauro daga jihar Adamawa da ya samar mata mataki na uku, da sakan 46, da digo 90.

Wakilin mu Aminu Halilu Tudun Wada, ya rawaito mana cewa an karkare gasar tare da bada Kofuna da kuma kyautar kudade ga wasu yan wasa da kuma jihohin da suka karkare a gaba -gaba.

Karin hotuna daga wurin taron rufe gasar:

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!