Connect with us

Labarai

Kwastam ta kama magungunan jabu masu ɗauke da lambar NAFDAC

Published

on

Hukumar yaki da fasa kyauri ta Najeriya Kwastam, ta kama magungunan jabu masu ɗauke da lambar rajistar NAFDAC ta bogin, miyagun ƙwayoyi da kuma magungunan da wa’adinsu ya ƙare, waɗanda jimillar ƙimarsu bayan biyan haraji ta kai Naira biliyan 53.39 a tashar jiragen ruwa ta Apapa da Legas.

 

Hukumar ta bayyana kamen a matsayin wani babban ci gaba a ƙoƙarinta na kare lafiyar al’umma da kuma tsaron ƙasa.

 

Da yake jawabi yayin miƙa waɗannan miyagun ƙwayoyi da magungunan da wa’adinsu ya ƙare ga hukumomin da abin ya shafa a hedikwatar rundunar Apapa a ranar Laraba, Shugaban Hukumar Kwastam ta Ƙasa, Bashir Adewale Adeniyi, ya ce an samu nasarar kama kayayyakin ne sakamakon tattara bayanan sirri da kuma haɗin gwiwa tsakanin Kwastam da NDLEA.

 

A cewarsa, kayayyakin da aka kama sun haɗa da sama da Tan 6.7 na tabar wiwi da aka ɓoye a cikin kwantena biyu masu ƙafa 40 tare da motocin da aka shigo da su da kuma kayan gyaran motoci.

 

Sauran abubuwan da aka kama sun haɗa da kwalabe 339,800 na maganin tari mai ɗauke da sinadarin Codeine, kwantenoni da dama na magungunan da wa’adinsu ya ƙare, maganin yara na Powder, da kuma magungunan jabu masu ɗauke da lambobin rajistar NAFDAC na bogi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!