Connect with us

Labarai

Shugaban Tinubu zai ƙaddamar da littafin tunawa da marigayi Muhammadu Buhari

Published

on

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zai ƙaddamar da wani littafin tunawa da marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a yayin bikin cikar shekara guda da rasuwarsa.

Shugaban Kwamitin Shirye-shiryen Taron kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya ce za a gudanar da addu’o’in ne a tsakanin mabiya addinin Musulmi da Kirista.

Boss Mustapha ya bayyana cewa littafin mai taken Tributes and Condolences in Honour of Muhammadu Buhari ya ƙunshi saƙonnin ta’aziyya daga shugabannin ƙasashe, jami’an diflomasiyya da fitattun jagororin siyasa daga sassa daban-daban na duniya.

Ya ce Shugaba Tinubu ne zai ƙaddamar da littafin, wanda daga bisani za’a dauki nauyin raba shi kyauta ga al’ummar kasa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!