Connect with us

Labarai

Shugaba Tinubu ya kaddamar da sauye-sauye a shirin NYSC

Published

on

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya kaddamar da wasu sabbin sauye-sauye ga shirin hidimar kasa NYSC, da nufin sabunta tsarin domin ya fi mayar da hankali kan bunkasa tattalin arziki da koyon sana’o’i da kuma inganta al’adun Najeriya.

Sabbin sauye-sauyen sun hada da rage mayar da hankali kan atisayen soja da aka saba yi a sansanonin hukumar ta NYSC, tare da kara horas da matasa kan sana’o’i da fasahar zamani da kasuwanci domin su samu damar dogaro da kansu bayan kammala shirin na hidimar kasa.

Haka kuma, gwamnatin ta ce, za a inganta sansanonin NYSC, tare da karfafa yin amfani da kayan gargajiya na cikin gida, a matsayin wata hanya ta bunkasa masaku da kuma kare al’adun Najeriya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!