Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kwastam ta saki tireloli 15 da ta kama makare da Hatsi

Published

on

Hukumar yaki da fasa kwauri Kwastam shiyyar Sokoto da Zamfara, ta bayar da izinin sakin wasu manyan motoci guda Goma sha biyar da ta cafke su makare da hatsi.

Hakan na cikin sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar na shiyyar, ya fitar.

Sanarwar, ta kuma buƙaci ‘yan kasuwa da su gaggauta sayar da hatsin a kasuwannin kasar nan.

BBC ta ruwaito cewa, Kwanturola Kamal ya sanar da kokarin hadin gwiwa tare da hukumar tattara bayanan sirri ta Kwastam CIU da kuma kungiyar hadin gwiwa ta JBPT domin sanya ido kan yadda ake rarraba wadannan hatsi a kasuwannin cikin gida, tare da tabbatar da cewa ba za su samu hanyar fita daga ƙasar nan ba ta hanyoyin fasakwauri.

Haka kuma, a cikin sanarwar, hukumar ta bayyana cewa ta saki Hatsin ne bisa bin umarnin da shugaban Bola Ahmed Tinubu ya bayar na inganta samar da abinci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!