Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

Gwamnatin Zamfara ta fitar da sabbin dokokin don magance matsalar tsaro

Published

on

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare, ya sanya hannu kan dokar haramta sayar da biredi maras  dauke da sunan kamfaninsa da ake naɗewa cikin leda da kuma hana sayar da fiye da lita 50 na man Fetur da kuma haramta amfani da gilashin mota mai duhu a jihar.

Gwamnan ya sa hannu kan dokar ne a Laraba makon nan a gidan gwamnatin jhar da ke birnin Gusau.

Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sulaiman Bala Idris, ya fitar.

Sanarwar ta ruwaito cewa dokar za ta yi maganin matsalolin da aka bayyana suna janyo ƙalubalen tsaro a jihar.

haka kuma ta cikin sanarwar ya kara da cewa an yi kaddamar da dokar ne saboda hare-haren baya-bayan nan da aka kai wasu yankuna a sassan jihar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!