Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kyan Hali: Ɗan jarida ya mayar da sama da miliyan guda da ya tsinta

Published

on

Wani ɗan jarida a jihar Gombe ya mayar da kuɗi har Dala dubu uku ($3000) da ya tsinta.

Ɗan jaridar mai suna Abdulƙadir Shehu Aliyu, ɗan asalin jihar Kano ne, kuma tsohon ma’aikacin Freedom Radio wanda ya ke aiki a gidan rediyon Progress FM, ya yi cigiyar tsuntuwar a gidan rediyo, inda daga bisani aka samu mai kuɗin.

Adadin kuɗin a Naira ya kama miliyan ɗaya da dubu ɗari biyu da ashirin da biyar da ɗari tara da tamanin N1,225,980.

A wani saƙo da ya wallafa a shafin sa na Facebook yayi godiya ga Allah inda ya bayyana cewa an samu mai kuɗin har ma ya karɓi abin sa.

Alhamdulillah, Alhamdulillah

Bayan Sanarwa da na bayar a gidan Radio Progress Gombe sakamakon tsintar kudi kimanin…

Posted by Prince Abdulkadir Aliyu Shehu on Thursday, April 29, 2021

Yanzu haka dai wannan labari ya fara ɗaukar hankalin jama’a a kafafen sada zumunta, ga na ra’ayoyin wasu daga ciki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!