Labarai
Kyautatawa malamai ya zama wajibi- Shekarau
Tsohon Gwamnan jihar Kano kuma Sanatan kano tsakiya a yanzu Malam Ibrahim Shekarau yace matukar anaso harkar Ilimi ta gyaru a fadin kasar nan ya zama wajibi Gwamnatocin jihohi su dauki gabarar gyara tsarin yadda Gwamnati ke daukar Malaman Makarantu.
Malam Ibrahim Shekarau wanda ya sami wakilcin Ahmad S Aruwa ya bayyana hakan ne lokacin bikin cikar kungiyar tsaffin daliban Kabo Old Girls Association KOGA aji na tamanin da tara shekara talatin da kafuwa.
Ahmad S Aruwa ya kara da cewa akwai bukatar tsaffin kungiyoyin Dalibai su rika kokarin kyautatawa Malaman da suka koyarda dasu domin ta sanadiyyar Malaman ne daliban suka zama wasu.
Rashin kwararru a bangaren ilimi ke kawo cikas – Tajudeen Gambo
Akwai karancin ilimin harkar fim ga masu shirya fina-finai
Kano zata hada kafada da kasashen duniya a bangaren ilimi –Ganduje
Alhaji Ahmad S Aruwa ya kuma shawarci sauran tsaffin daliban Makarantu dasuyi koyi da irin kokarin da kungiyar ke yi musamman wajen taimako da sada zumunci.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito an gudanar da makaloli dake nuni da muhimmancin zumunci kamar yadda yake a cikin addinin Musulunci.