Labarai
Labari mai daɗi: Mutane 50,000 za su amfana da tallafin Corona a Kano
Gwamantin jihar Kano tace bata amince wata ƙungiya daga wata jiha tazo Kano don yin rijistar shiga tsarin da gwamnatin tarayya ta fito da shi na tallafin raɗaɗin Corona ga masu ƙananan sana’o’i da malaman makarantu masu zaman kansu.
Shugaban ofishin da ke kula da tsare tsare-tsare da aiwatarwa na jihar Kano Rabi’u Sulaiman Bichi ne ya bayyana hakan a yau yayin zantawa da ƙungiyoyi a ofishinsa.
A nasa ɓangaren mai bai wa gwamnan Kano shawara kan harkokin masu gyaran ababen hawa Injiniya Idris Hassan yace, kowacce ƙungiya za su zaɓo mutane 450 da za su amfana da tallafin.
Mataimakiyar shugabar ƙungiyar makarantu masu zaman kansu Maryam Magaji ta ce malaman makarantun su Dubu Sha bakwai ne za su amfana da tsarin.
Wakiliyar mu Zahra’u Nasir ta rawaito cewa Rabiu Sulaiman Bichi ya ƙara da cewa in aka aiwatar da shirin mutum dubu hamsin ne ake tsammanin zasu amfana da shirin anan Kano.
You must be logged in to post a comment Login