Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Labari mai dadi: Ba a samu wanda ya kamu da Corona ba a Kano ranar Alhamis

Published

on

Kididdigar da cibiyar dakile cutuka masu yaduwa ta kasa NCDC ta fitar a daren Alhamis da misalin karfe 10:20 ta nuna cewa babu ko mutum daya da ya kamu da kwayar cutar Corona a Kano.

Kididdigar ta ce jihar Kano ta samu karin mutum 5 akan kididdigar hukumar ta ranar Laraba wadda tace Kano na da mutane 16, idan aka hada Kano tana da mutane 21 masu dauke da cutar.

Sai dai tun a daren Larabar da ta gabata ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta sanar da karuwar adadin a shafinta na Twitter inda ta tabbatar da cewa Kano na da mutane a 21.

Sanarwar da hukumar NCDC ta fitar ta ce yanzu haka adadin wadanda suka kamu da cutar sun kai mutane 442, daga ciki mutane 152 sun warke, yayin da 13 daga ciki suka rasa ransu.

Har izuwa 12 na dare, ma’aikatar lafiya ta jihar Kano bata fitar da sanarwa kan Corona ba, sai ma kara wallafa kididdigar hukumar NCDC ta yi a shafinta na Twitter.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!