Coronavirus
Covid -19:Kungiyar likitocin dabbobi ta bada tallafi
Kungiyar likitocin dabbobi, ta kasa reshen jihar Kano, ta bada gudunmowar kayan wanke hannu a wani mataki na kokarin dakile yaduwar cutar Corona Virus, a fadin jiha da kasa baki daya.
Da yake jawabi lokacin mika tallafin shugaban kungiyar likitocin dabbobi Dakta Abubakar Sani Inuwa, ya ce sun bada tallafin ne don agazawa kokarin gwamnati na magance cutar covid 19 a jihar kano.
A nasa bangaren daraktan hukumar kula da magunguna da bada su, na jihar Kano kuma shugaban kwamitin karbar tallafin magunguna na cutar covid 19 da gwamnati ta kafa kan tallafawa al’umma, pharmacist Hisham Imamuddeen, ya bukaci mawadata su tallafawa marasa karfi musamman ma a lokaci irin wannan.
Labarai masu alaka.
Covid-19: Ganduje zai fara raba tallafin kayan abinci
Covid 19- Fitilar Bichi ta raba kayan tallafi
Hisham Imamudden, ya bukaci hakan ne jim kadan bayan karbar tallafin da kungiyar likitocin dabbobi suka bayar na sinadarin wanke hannu ‘Hand Sanitizer’ guda dari biyar ga kwamitin domin rabawa al’umma mabukata.
Bilal Nasidi Mu’azu, wakilinmu da ya halarci taron rabon yace kungiyar ta gudanar da feshin magani a gidan namun daji dake nan kano tare da raba sinadarin wanke hannu guda dari uku.
You must be logged in to post a comment Login