Labarai
Laifin iyaye ne ke haifar da mace-macen aure -Hisbah
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta alakanta matsalar mace-macen Aure a yanzu da rashin sauke hakkin da Allah ya dorawa mazajen ta bangaren kula da yalansu.
Babbar kwamandan hukumar ta Hisba bangaraen mata Malama Ummulkulsum Kasim ce ta bayyana hakan, bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan tashar freedom radiyo da ya mayar da hankali kan yadda za’a magance matsalolin aure cikin wannan al’umma.
Malama Ummulkulsum ta kara da cewa, mafi yawan gurbacewar tarbiyyar ya samo asali ne daga rashin kyakkyawar alakar Aure tsakanin iyaye wanda hakan ke sanya yaran su rasa kulawar da ta dace daga iyayensu.
Hisbah ta cafke matashi kan yunkurin haikewa budurwar abokinsa
Hukumar Hisbah ta kama mabarata anan Kano
A nata bangaran wata matashiya da ta kasance cikin shirin kuma take wakiltar ‘ya ‘ya mata Hauwa Shuaibu Gaya, ta alakanta matsalar da ake samu a zamantakewar Aure da cewa rashin tarbiyya ne da ake samu tun daga gida kafin ma ayi Aure.
Bakin biyu sun yi kira ga iyaye maza da mata da su rika kula da yadda zasu tsara zamantakewar auren su domin tabbatar da samar da tarbiyya ta gari ga zuriar su.